Alhamis 29 Oktoba 2026 - 23:20
Ku Ɗauki Makaman Ilimi, Imani da Tarbiyyar Kai Domin Gina Makoma

Hauza/ Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i (DZ), ya yi kira ga matasa da ɗalibai da su ƙarfafa kansu da ilimi, imani, tarbiyyar kai da kusanci da Allah, tare da zurfafa fahimtar koyarwar Alƙur’ani da Ahlul Baiti (AS), domin taka rawar gani wajen gina makoma da ƙara wa Iran ƙarfi.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a cikin saƙonsa ga matasa da ɗaliban da suka aiko masa da wasiƙun ƙauna da goyon baya, Jagoran ya bayyana godiyarsa bisa kulawa da ƙaunar da suka nuna masa, tare da alƙawarin yi musu addu’o’i na musamman.

Ga fassarar cikakken saƙon na Jagoran

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai

Assalamu alaikum, ya ku ’ya’yana ababen ƙauna!

Na karanta wasiƙunku masu cike da ƙauna. Ina godiya gare ku, ɗalibai matasa masu ƙwazo da himma, bisa irin ƙauna da kulawar da kuka nuna mini. Zan keɓe addu'o'i na musamman gare ku baki ɗaya, waɗanda kuka ɗora mini haƙƙi a kanku.

A cikin wasiƙunku, da kuma na wasu matasa da ɗalibai da dama waɗanda suke nuna mini ƙauna da kulawa, ina ganin ƙuduri, azama da jin nauyin alhakin gina makoma suna haskakawa.

Wannan ƙaƙƙarfan alƙawari amana ce mai matuƙar daraja. Tana da tushe a makarantar tunanin Musulunci na gaskiya da Annabi Muhammad (SAWA) ya zo da shi, da kuma gadon Imam Khumaini Mai Girma da Shahid Khamene'i (Allah Ya ɗaukaka matsayinsu). Wannan alƙawari shi ne igiyar da ta haɗa mu da juna wajen kasancewa masu manufa ɗaya da cika alƙawarin da muka ɗauka.

Domin cimma wannan manufa, ku yi iya ƙoƙarinku wajen tanadar wa kanku makaman ilimi, imani, tsarkake zuciya da ɗabi'u, kusanci da Allah, da zurfafa fahimtar koyarwar Alƙur'ani da Ahlul Baiti (AS).

Haka kuma, ku ƙara ƙoƙari da ƙirƙire-ƙirƙire a cikin ayyukanku domin ƙara wa ƙasarmu ƙaunatacciya ta Iran ƙarfi da ƙarfin iko.

Ta haka, da addu'ar Shugabanmu mai tausayi, Imam Mahdi (AF), za a samu kyakkyawan ci gaba da sauri wajen tafiyar da rundunar masu alƙawari tare, zuwa kololuwar ci gaba da wayewar Musulunci da Iran, in Allah Ya yarda.

Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i 

6 ga Aban (28 ga Oktoba, 2026).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha